Labarai
Kungiyar kwallon kafa ta Ashafa Action ta lashe kofin Tofa Premier
A wasan karshe na gasar cin kofin firimiya na jihar Kano watau Tofa Premier, da aka kammala a yammacin Talatar nan, kungiyar kwallon kafa ta Ashafa Action dake Gwauron Dutse, ta zama Zakaran gasar bayan da ta doke abokiyar karawarta ta Kano Lions.
Tunda fari an tashi wasan kowace kungiya na nema kafin daga bisani Ashafa Action ta samu galaba da ci 3- 2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Wasan dai ya samu halartar dumbin jama’a ciki kuwa har da masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen Jihar Kano.
Da yake jawabi Jim kadan bayan kammala wasan Hakimin Tofa Dan Adalan Kano, Alhaji Isyaku Umar Tofa, ya bayyana jindadin sa bisa ga yadda gasar ta kammala cikin nasara ba tare da samun matsala ba.
A nasa bangaren mai horas da kungiyar Ashafa Action,Nafiu Ogaba,ya yabawa ‘yan wasan kungiyar tare da nuna jin dadin sa da samun nasarar da kungiyar tayi.
Da yake Tofa albarkacin bakin sa,shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kano Alhaji Sharu Rabiu Inuwa Ahlan, ya yi kira ga masu hannu da shuni da kamfanoni masu zaman kansu,da su zo a hada hannu dasu don tallafawa harkar kwallon kafa a Jihar Kano.
Kungiyoyi 24 ne dai suka fafata a gasar wanda aka raba zuwa rukunin A da kuma B, Nasiru Aminu na kungiyar Ashafa Action ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zura kwallayewanda ya zura kwallaye 11,sai mai tsaron gida na kungiyar kwallon kafa ta Dabo Feeder, Sani Alhasan wanda ya zama mai tsaron raga mafi hazaka a gasar.