Labarai
Kungiyar lauyoyi ta yaba wa Gwamnan Kano bisa umarnin bincikar zargin belin Danwawu

Kungiyar lauyoyi NBA reshen Ungogo, ta yaba wa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, bisa kafa kwamitin bincike domin bincika zargin da ake yi wa kwamishina Ibrahim Namadi na ya tsaya wa wani da ake zargin babban Dillalin miyagun kwayoyi ne da ya ke fuskantar shari’a a babbar kotun tarayya da ke Kano.
Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Ahmad Abubakar Gwadabe, ƙungiyar ta bayyana matakin da gwamnan ya dauka a matsayin na gaggawa da jajircewa, inda ta bayyana cewa hakan na nuni da gagarumin kudurinsa na magance laifukan da suka shafi muggan kwayoyi.
Haka kuma, kungiyar ta NBA ta nuna matukar damuwarta kan wannan zargin, inda ta yi gargadin cewa duk wani nau’i na hadin gwiwa a hukumance a cikin safarar miyagun kwayoyi ya na lalata doka da oda tare da yin barazana ga tsaron jama’a.
Sanarwar ta kara da cewa, “Laifuka masu alaka da muggan kwayoyi suna da alaka da karuwar rashin tsaro da gurbata matasa, da kuma yawan munanan dabi’u.
Yayin da suke yaba wa amiyar gwamnan, lauyoyin sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da gudanar da bincike a fili ta hanyar bayyana sakamakon binciken kwamitin.
Kungiyar ta kuma bukaci mambobin kwamitin binciken da su gudanar da aikinsu cikin kwarewa da gaskiya da rashin son kai, ko da yake ba a bayyana sharuddan binciken ba.
Reshen na Ungogo na kungiyar lauyoyin, ya jaddada kudirinsa na tabbatar da adalci da kare muradun jama’a, tare da yin alkawarin ci gaba da bayar da goyon baya ga kokarin tabbatar da doka da oda da kuma yaki da yaduwar miyagun kwayoyi a jihar Kano.


You must be logged in to post a comment Login