Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar lauyoyin reshen jihar Kano ta nesanta kanta daga rufe kotuna na kwanaki 2

Published

on

Kungiyar lauyoyi reshen jihar Kano NBA ta nesanta kanta daga rufe kotunan na kwanaki biyu da za’a fara daga yau Talata, don yin biyayya ga umarnin uwar kungiyar ta kasa,a wani mataki na nuna kin goyan bayan matakin dakatar da babban joji na kasar nan Walter Onnoghen.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da sakataren kungiyar ta Kano Mujtaba Adamu Ameen ya fitar cewa, ba zamu hana wani manba na kungiyar NBA hana zuwa kotuna ba, yana mai cewa ya zama wajibi kungiyar ta goyi bayan yaki da cin hanci da rashawa.

Barrister Mujitaba Adamu ya kara cewar abunda ya rataya a wuyan kungiyar shi ne don tabbatar da cigaban kasar nan da ma ‘yan Najeriya.

Haka zalika sakataren kungiyar ya kara da cewar,kamata yayi lauyoyi su dinga girmama kwarewar su, wajen tabbatar da adalci ga al’umma da ‘ya’yan mu da ma wadanda ba su zo duniya ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!