Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar JAMB: Dalibai 869,709 ne suka yi rijista don jarabawar watan Maris

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da Sakandire ta kasa (JAMB) ta ce dalibai dubu dari takwas da sittin da tara da dari bakwai da tara ne suka yi rajista domin rubuta jarabawar wannan shekara da za a yi a watan Maris.

Hakan na kunshe ne cikin rahoton da hukumar ke fitarwa a mujallarta na mako-mako.

Hukumar ta JAMB ta kuma ce ta soke wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar guda tara sakamak on karya ka’idoji da su ka yi.

Rahoton na hukumar JAMB ya kara da cewa, cibiyoyin da aka soke lasisin su, sun bukaci kudade fiye da adadin da gwamnati ta ayyana.

Haka kuma hukumar JAMB ta ce ana ci gaba da binciken wasu cibiyoyi guda goma da ke jihohin Lagos da Filato.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!