Labarai
Kungiyar lauyoyin ta kasa reshen jihar Kano, ta nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar laifukan take hakkin dan Adam

Kungiyar lauyoyin ta kasa reshen jihar Kano, ta nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar laifukan take hakkin dan Adam tare da yin kira da a kara bin doka da oda a daidai lokacin da kasar nan ke bikin ranar dimokkuradiyya.
Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar a nan Kano Usman Umar Fari.
Usman Umar ya jaddada cewa, akwai bukatar hukumomin da abin ya shafa su kara sanya idanu don ganin an kawo karshen karuwar laifukan take hakkin dan Adam a kano dama kasa baki daya.
You must be logged in to post a comment Login