Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar likitocin masu neman kwarewa a Najeriya sun janye daga yajin aikin da suka shiga

Published

on

Kungiyar likitocin masu neman kwarewa a Najeriya NARD sun dakatar da yajin aikin sai baba-ta-gani da suka fara a ranar 26 ga watan Yulin data gabata.

Shugaban kungiyar na kasar Dr Innocent Orji ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja, ta hanyar sakon Whatsapp da ya aika ga manema labarai.

A cewarsa, nan da makonni biyu kungiyar zata sake duba lamarin.

Dr Innocent Orji ya kuma ce “mun dakatar da yajin aikin ne kawai, za kuma mu ci gaba da aiki da karfe 8 na safiyar Asabar, 12 ga Agusta.

“inda kuma za mu sake nazarin ci gaban da aka samu nan da makonni biyu.”

Hakan dai na zuwa ne bayan da wasu masu ruwa da tsaki na kungiyar suka duba yiwuwar cigaba da yajin aikin, ko kuma janyewarsa.

Haka zalika kungiyar ta duba kiran da kakakin majalisar wakilai ta kasar Hon.Tajudeen Abbas yayi na kira ga kungiyar data daure ta janye daga yajin aikin data shiga, duba da cewa wannan gwamnatin har yanzu bata gama zama daram akan kukera ba. wanda ya ce majalisar na cigaba da duba hanyoyin da za’abi a shawo kan matsalar likitocin, duk kuwa da cewa har ya zuwa yanzu minitocin kasar basu kama aiki ba.

Duk kuwa da cewa a baya kungiyar, baya ga yajin aikin data shiga, tayi ikrarin shirya zanga-zanga tare da kwalejojin kiyon lafiya da ma’aikatar lafiya ta tarayya.

Sai dai kuma bayan shiga tsakani da fadar shugaban kasa da shugaban majalisar dattawa suka yi, an dakatar da zanga-zangar.

ruhotanni sun nuna cewa mambobin kungiyar sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani ne don biyan bukatun kansu.

Wasu daga cikin bukatun sun hadar da ‘yin bitar Ƙarfafa Tsarin Albashi na Likita (CONMESS) daidai da cikakken albashin dai-dai da na shekarar 2014 na CONMESS da kuma biyan bashin sakamakon daidaita mafi ƙarancin albashi ga likitocin da aka tsallake’.

NARD ta ce’manyan bukatun kungiyar su ne: biyan kudi nan take na Asusun Horar da likitoci masu neman kwarewa (MRTF) na shekarar 2023 da dai sauransu’.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!