Labarai
Zulum ya raba kayan tallafi ga iyalai dubu 300 a Borno
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya raba tallafin abinci da sauran kayan buƙata ga mutune 2,000 a unguwar Feezan a jihar.
Gwamnan ya yi Rabon tallafi ne a wani yunkuri na ragewa al’umma radadin janye tallafin man Fetur da Gwamnatin tarayya tayi.
Ko a watan Yulin da ya gabata gwamna Zulum ya ƙaddamar da shirin bayar da tallafin da nufin taimakawa iyalai dubu 300.
Kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautun jihar Borno, Sugun Mai Mele, ya ce unguwanni 15 ne za su amfana da wannan tallafi a jihar.
Rahoton: Yusuf Sulaiman Ahmad
You must be logged in to post a comment Login