Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rushewar wani masallacin jumma’a a Zariya yayi sanadiyar rasa rayuka

Published

on

Ana fargabar mutane da dama sun mutu a babban Masallacin Zariya na Jihar Kaduna da ke ƙofar fada, bayan ruftawar ginin mai tsohon tarihi na Masarautar Zazzau.

Wata majiya daga fadar Sarkin Zazzau ta ce ‘har lokacin da aka hada wannan rahoton ana ci gaba da aikin ceto al’umma, bayan aukuwar lamarin a ranar Juma’ar’.

Rahotanni sun ce rufin wanda na ƙasa ne ya rufta ya fado ne a lokacin da ake gudanar da Sallar La’asar din yammacin jumma’at.

 

Babu cikakken bayani a yanzu kan yadda lamarin ya faru.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna mutane ɗauke da shebura suna yashe ƙasar da ta rufta a tsakiyar masallacin.

An kuma ga wani da ke nuna yadda rufin ginin a wani sashe na tsakiyar masallacin ya ɓare har ana iya hango sama a lokacin da aikin ceton ke ci gaba da gudana.

 

BBC ta rawaito Masallacin, tsohon gini ne da aka yi shi cikin fasali irin na gine-ginen Hausawa da yawan ginshiƙai da ke tashi daga jikin ganuwa har zuwa rufin ginin, sannan su tanƙwara su sauka a ɗaya ɓangaren

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!