Kiwon Lafiya
Kungiyar miyatti Allah Kautal-Hore ta musanta zargin da ake yiwa makiyaya a Benue
Kungiyar miyatti Allah Kautal-Hore ta musanta zargin da ake yiwa Fulani makiyaya na kisan mutanen da aka yi a Jihar Benue.
Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Bello Abdullahi Bodejo ne ya bayyana hakan Alhamis din nan, yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta yi a nan kano, inda ‘’ya ce ko kusa ko alama Fulani makiyaya basu da hannu a cikin rikicin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama’’.
Bello Badoje ya kuma ce ‘’tunda ake rikici a jihar ta Benue ba’a taba kama wani bafillatani da hannu dumu-dumu ba a cikin kashe-kashen da ake yi illa ma fulanin da ake yiwa kisan gilla’’.
Badoje ya kuma ce a ‘’kwanakin baya an kama wasu mutane da makamai wadanda ake zargin suna daga cikin masu tada fitina kuma sun bayyana cewa gwamnatin jihar Benue ce ta basu domin aikata ta’addanci, sai dai tun daga wancan lokaci kawo yanzu ba’a kara jin an tada maganar ba’’.
Ya kuma ce idan aka yi la’akari da hotunan da aka rika yadawa a kafafen sada zumunta na wadanda aka kama da makamai da ake zarginsu da tada fitina a sassan jihar, za’a tabbatar da cewa, ko da mutum daya babu bafulani a cikinsu, kuma babu wani Bafulatani da ke da bindiga kirar AK47.
kungiyar ta ce a shirye take take don zama da gwamnatin jihar ta Benue domin lalubo bakin zaren fituntunin da ake yawan samu a jihar kuma ake alakanta shi da fulani.
Haka zalika shugaban kungiya ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar shiga cikin lamarin don kawo gyara ta hanyar tsaurara tsaro a jihar.