Labarai
Kungiyar tarayya EU zata taimakawa Najeriya da fiye da Euro miliyan dari hamsin
Kungiyar tarayyar Turai ta ware fiye da Euro miliyan dari da hamsin domin tallafawa Najeriya wajen inganta sauyin yanayi
Jakadan kungiyar tarayyar Turai Ketil Karlsen ne ya bayyana haka yayin wani taron sauyin yanayi da aka gudanar a jami’ar Bayero ta Kano da hadin gwiwar kungiyar tarayyar Turai.
Jakadan kungiyar tarayyar Turai Ketil Karslen ya ce lokaci yayi da za’a dara daga kan turban samar da tsare-tsare zuwa ga aiwatar da su, inda yake cewa a yanzu kungiyar ta tarayyar Turai zata fi maida hankali ne wajen aiwatar da tsare-tsare da aka riga aka fito da su a aikace.
Ya ce yana da matukar muhimmanci yin hubbasa wajen inganta shirye-shiryen muhalli musammam matalolin da suka dangance sauyin yanayi da amfani da makamashi,ta hanyar amfani da wasu daga cikin abubuwa da ake amfani da su kamar su kashin shanu, shara dangogin tukkan rake,shara kamar na su takardu da sauransu wajen samar da makamashin da ba zai gurbata muhalli ba.
Ya kuma ce kungiyar tarayyar turai zata taimaka wa Najeriya wajen samar da kaidoji da hanyoyin magance matsalar sauyin yanayi, inda yake cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da suke fama da wannan matsala ta sauyin yanayi, tare da cewa ita ce kasar da ta fi kowacce girma a nahiyar Afrika.
Tuni kungiyar tarayyar EU ta fitar da kudi Euro miliyan 150 kan matsalolin sauyin yanayi da hanyoyin amfani da yanayi na hasken rana, da saura makamashin da muke samarwa a harkokin yau da kullum domin samar da makamashin da baya cutarwa ga yanayi mu
Tare da magance matsaloli na noma, kwarowar Hamada da samar da hasken lantarki.
Ketil ya ce a nan da sheraka ta 2030 akwai bukatar ganin ruwan sha ya wadata a Najeriya baki daya a wani yunkurin taimaka mata kamar yadda yake a kundin tsarin majalisar dinkin duniya na kasashen da suka cigaba su taimakawa kasashe masu tasowa wajen samar da wasu ababa more rayuwa.
Ko a nan Kano kungiyar ta EU na yunkurin samar da kudirori da tabbatar da irin wadanan matsaloli da ke adabar jihar mussamam matsala ta bahaya a bainar jama’a ,tsaftace muhalli da kawar da kwarorwar Hamada na daga cikin tsare-tsarensu.
Ya kuma ja hankali yan jihar Kano da su sani cewar babu wata al’umma da take cigaba face sai da zaman lafiya, sannan ya yaba da yadda al’ummar jihar Kano ke kokarin tabbatar da zaman lafiya, hakan ce ma ta sa ba’a samu barkewar rikce-rikce kamar yadda ake samu a Arewa maso gabashin Najeriya.