Labarai
Kungiyar tarayya Turai zata kasha sama da miliyan 140 don tallafawa jihar Borno
Kungiyar tarayyar turai EU ta ce za ta kashe yuro miliyan dari da arba’in da uku kwatankwacin sama da naira biliyan sittin domin tallafawa gwamnatin jihar Borno wajen aiwatar da wasu muhimman ayyuka tara wadanda zasu taimaka wajen farfado da komadar jihar da ke tsaka mai wuya sakamakon rikicin ‘yan tada kayar baya.
Da yake kaddamar da ayyukan, babban jami’in tarayyar Turai Kurt Cornelis, ya ce za a baiwa kungiyoyin jin kai na duniya da ke gudanar da ayyuka a jihar ne kudaden domin su aiwatar da shirin.
Mr Kurt Cornelis, ya kuma ce kungiyoyin da za su kula da ayyukan sun hada da: Action against Hunger da Alima da DFID da FAO da IRC da Mercy Corps da Norwegian Refugee Council da kuma hukumar bunkasa kasashe na majalisar dinkin duniya UNDP.
Ya kara da cewa kudaden za su taimaka gaya wajen sake farfado da jihar wanda rikicin ‘yan Boko-haram ya daidaita a baya-bayan nan.
A cewar sa wannan shine karo na uku da tarayyar turai ke ware makudan kudaden domin gudanar da ayyuka a jihar ta Borno cikin shekara guda.