Labaran Kano
Kungiyar Tifa ta gina gada a Kano
Kungiyar direbobin Tifar yashi ta jihar Kano reshen kwanar Tifa ta gina wata katafariyar Gada a Karamar hukumar Nasarawa domin ragewa gwamnati nauyin dake kanta.
Shugaban Kungiyar Direbobin Tifar yashi ta kasa shiyyar Kano Kwamared Mamuni Ibrahim Takai ne ya shaida hakan a yau lokacin bikin bude katafariyar Gada da reshen Kwanar Tifa suka gina daya gudana a yau.
Mamuni Ibrahim Takai yace ‘yan kungiyar sun dauki matakin sake gina gadar ne ta Kwanar Tifa bayan karyewa da gadar tayi domin su ragewa Gwamnati aiki da kuma taimakawa mazauna yankin baki daya.
Shugaban kungiyar Mamuni Takai ya kuma yi kira ga sauran mambobin kungiyar dasu rika gudanarda ayyukan alkairi a yan kunansu domin ciyarda yan kunan nasu gaba ta kowacce fuska.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito shugaban Kungiyar reshen Kwanar Tifa Yahya Sadi Adamu na yabawa sauran mambobin kungiyar bisa namujin kokarinda suke yi, inda kuma kara tabbartar da cewa zasu cigaba gudanarda ayyukan alkairi a unguwar.