Connect with us

Labaran Kano

Kungiyar ‘yan tifa ta musanta rashin birkin motocinta

Published

on

Kungiyar Direbobin Tifa ta kasa reshen jihar Kano ta ce ko wace motar tifa dake dibar yashi a Kano tanada cikakken burki, ba kamar yadda wasu ke zargin babu ba.

Kungiyar tace yawaitar korafin samu afkuwar hadura a inda direbobin motar ya rutsa dasu ko kuma makamancin haka a fadin jiha ya jawo yawaitar cecekuce akan motocin da direbobin su.

Hakan ya sa al’umma da dama ke zargin cewa rashin birki ke  haddasa  samun hadura a titunan jihar Kano.

Shugaban kungiyar direbobin Tiffofi  ta kasa reshen jihar Kano Kwamred Mamuni Ibrahim Takai, ne ya tabbatar da hakan lokacin bude bita ga direbobin tifar yashi na Kano wanda kungiyar ta shirya da hadin gwiwar hukumar lura da ababen hawa  VIO reshen jihar Kano da kuma Ma’aikatar gidaje da sufuri ta Kano.

labarai masu alaka.

Ana zargin KAROTA da haddasa hatsari a titin Zariya

 

Mamuni Ibrahim, ya ce gudun wuce sa’a da wasu direbobin tifar ke yi ke haddasa  hatsarin da ke sa  ba’a iya shawo kan tifar da wuri da hakan ke saka shakku a zukatan al’umma  cewar motocin basu da birki.

Mamuni Ibrahim,  ya tabbatar da cewa a halin yanzu mafi yawa daga cikin direbobin Tifofin  na amfani ne da sabbin motoci na zamani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!