Labarai
Kungiyoyi sun yi zanga-zanga a Kano
Gamayyar kunigiyo masu zaman kansu a nan jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana yau juma’a a nan Kano domin nuna takicinsu kan yadda yan jaridu suka yi shiriu da batun yaran da aka sace a ka kai jihar Anambra aka kuma mayar da su kirista.
Gamayyar kungiyoyin sun yi tattakin ne yau a nan Kano inda suke dauke da rubutu da ke nuna yin Alawadai da al’amarin tare da zarigin yan jaridu da kuma gwamnati da yin guma da bakin su.
Guda daga cikin masu zanga-zangar Shazali Abubakar Adamu ya shaidawa freedom Radio cewar sun fito zanga-zangar ne domin nuna adawa da satar yaran aka kuma mayar da su kirista, amma gwamnatoci suka yi shiru.
Satar yaran Kano da munafurcin kafafan yada labarai
Yaran Kano: Majalisar dokokin Kano zata dauki mataki
An siyar da ‘ya ta naira Miliyan Daya da rabi
Shima da yake nasa jawabin ga dandazon masu zanga-zangar Bashir Usaini kira yayi da babbar murya ga mahukunta da su fito su magantu su kuma dauki matakin gaggawa kan al’amarin
Haka shima Sagiru Alhansan ya kalubalanci kafafen yada labarai da sauran jama’ar gari kan nuna halin ko in kula da jama’a sukayi kan al’amarin yana mai cewar abu ne da yakamata jama’a su hada hannu wuri guda.
Kungiyoyi da dama ne dai suka fito daga nan jihar Kano suka kuma hadu wuri guda domin gudanar da zanga-zangar ta lumana damin jan hankalin gwamnati da ta mayar da hankali kan al’amari.