Kasuwanci
Kungiyoyin kishin yan Nijeriya sun maka CBN a Kotu
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da sa ido kan harkokin hada-hadar kudaden al’umma SERAP da takwarar ta, ta bibiyar kudaden kasafi ta BudgIT da ta kuma kungiyar 136 concerned Nigerians, sun maka Babban bankin kasa CBN a Kotu, kan tuhumar sa da ya ayyana sabon tsarin tsaron Internet na kudaden al’umma da ke asusun ajiyarsu.
Kungiyoyin dai sun maka CBN a kotu ne saboda wani umarnin bankin na baya-bayan nan wanda ya umarci dukkan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi da su cire harajin tsaron watau Cybersecurity levy kimanin kashi 0.5 cikin 100 akan duk wata hada-hadar kasuwanci ta yanar gizo.
Umarnin, wanda aka bayar a ranar 6 ga Mayun bana, masu shigar da kara sun yi wa karar ta su da lakabi Umurni ba bisa doka ba.
A cewar Kolawole Oluwadare, mataimakin daraktan SERAP, cirewa mutane ‘yan kudadensu daga asusun ajiyarsu, ya zarce ikon babban bankin na CBN.
Sai dai kai karar Kotun na zuwa ne bayan da Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya bada umarnin dakatar da daukar kudin kafin zuwa watan Satumba.
You must be logged in to post a comment Login