Labarai
Kungiyoyin kwadago da Gwamnati za su sasanta
Gamayyar kungiyoyin kwadago da kuma bangaren gwamnatin tarayya da Suka cimma matsaya kan yadda tsarin amfani da sabon mafi karancin albashin ma’aikata zai kasance za su gana da mambobinsu na jihohi a ranar Talata mai zuwa a birnin tarayya Abuja, don duba yadda tsarin zai kasance a Jihohi.
Sakataren gamayyar kungiyoyin da kuma tsagin gwamnati Alade Lawal neya sanar da jiya laraba yayin zantawa da manema labarai, yana mai karin
hasken cewa za su dauki gabaren horas da na Jihohin yadda za su cimma matsaya da gwamnoninsu.
Bayan cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya kan yadda tsarin zai kasance a tarayya, ana sa ran cimma makamanciyar wannan yarjejeniya a Jihohi, inji Alade Lawal.
Ya kuma kara da cewa gamayyar kungiyar kwadago ta kasa da bangaren gwamnatin tarayya za su sanya idanu kan yadda na jihohin za su tattauna batun, sannan idan har har akwai bukatar su sanya baki a cikin tattaunawar to za su yi.
A farkon makonnan nan ne dai gwamnonin Jihohon kasar nan karkashin kungiyarsu ta NGF suka gudanar da wata ganawa a Abuja, inda suka cimma matsayar cewa amfani da sabon tsarin ga ma’aikatan da albashinsu ya zarta naira dubu talatin zai dogara ne ga karfin tattalin arzikin ko wace.
Naira dubu talatin zai dogara ne ga karfin tattalin arzikin ko wace Jiha.