Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyoyin kwadago za su nazarci karin farashin mai da wutar lantarki

Published

on

Ministan kwadago da samar da aikinyi, Dr Chris Ngige ya ce, za su zauna yau Asabar da gamayyar kungiyoyin kwadago kan batun karin farashin kayayyaki sakamakon karin farashin wutar lantarki da na man fetir da aka samu a baya abayan nan.

Dr Chris Ngige ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayyan wata ganawa da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari jiya a fadar sa.

Ya ce, a zaman da za su yi a yau Asabar, zai mayar da hanakali don nazartar tattalin arziki da kalubalen da ya janyo tashin farashin kayayyaki a kasar nan.

Chris Ngige ya ce, ko a zaman su na jiya da kungiyar kwadago ta NLC da TUC sun yanke hukuncin sake zama a yau don samo bakin zaren.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!