Labarai
Kungiyoyin manoma ku biya bashin da ake bin ku -CBN
Babban bankin kasa CBN ya yi kira, ga Kungiyoyin manoman Auduga wadanda suka cigajiyar samun bashi na tsarin shirin bada rance ga manoma da su yi kokarin dawowa da bankin rancen da suka karba, domin baiwa sauran manoma damar karbar wani bahi a nan gaba.
Shugaban Bankin a nan Kano Alhaji Ali Abdulkadir ne ya bayyana hakan yayin taron da kungiyar Manoman Auduga ta kasa shiyyar Kano ta shirya na kaddamar da fara karban biyan bashin da aka baiwa manoman a shekara ta 2019.
Alhaji Ali Abdulkadir ya kara da cewa kamata yayi manoman su ji tsoron Allah su dawo da rancen da aka basu domin an tsara shirin ne domin tallafawa harkar noma tare da bunkasa shi domin ci gaban manoma a kasar nan.
Za’a dawo da ma’aikatun casar Shinkafa a Kano -Nanono
RIFAN: ta bayyana matakan da manoma za su karbi bashi
EFCC shipyard Sokoto ta kama shugaban kungiyar manoman shinkafa na karakamar hukumar Gumi
Da yake jawabi a yayin taron Alhaji Sai’du Dattijo Adahama cewa yayi babban abunda ke ci wa masu kamfanonin masaku tuwo-a-kwarya anan Kano shi ne bai wuce rashin aiwatar da bukatarsu a majalisar dokoki ta Kano ba wajen siyan kayayyakin da suke noma maimakon shigowa da shi daga kasashen waje, amma yaci tura.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa mambobin kungiyar manoman Auduga da dama ne suka halarci taron daga ko ina a kananan hukumomin jihar Kano 44 domin biyan bashin da suka karba daga wajen bankin na CSN.