Labarai
Kungiyoyin SSANU da NASU sun tsunduma yajin aiki
Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in ta Nijeriya SSANU da takararta ta ma’aikatan da ba malamai ba NASU sun tsunduma yajin aikin gama gari a wani mataki na nuna rashin amincewarsu da abin da suka bayyana a matsayin rashin adalci da kuma sabani na biyan albashi da gwamnatin tarayya ke yi.
BBC ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar SSANU Mohammed Ibrahim, ne ya tabbatar da fara yajin aikin a shirin gidan Talabijin na Channels, inda ya bayyana cewa ma’aikata a sassan jami’o’i daban-daban sun shiga yajin aikin.
Ya kuma jaddada cewa wannan mataki zai ci gaba har tsawon kwanaki bakwai masu zuwa matukar gwamnati ba ta magance kokensu ba.
Ya bayyana rashin jin dadinsa game da rashin samun hanyar sadarwa a hukumance daga wakilan gwamnati.
Ya bayyana damuwarsa game da yiwuwar masu zagon kasa a cikin gwamnati, yana mai tambayar dalilin da ya sa wasu jami’ai ba su cika umarnin shugaban kasa Bola Tinubu na biyan alawus-alawus na 2022 ga mambobin kungiyar jami’o’i ba.
Haka kuma shugaban ya soki Ministan Kwadago Nkiruka Onyejeocha bisa gazawa wajen tuntubar kungiyoyin kwadagon duk da cewa ya samu sanarwar kwanaki bakwai da suka bayar na shiga yajin aikin a ranar Litinin da ta gabata.
You must be logged in to post a comment Login