Labarai
Kwalejin kimiyya da fasaha zata gurfanar da gwamnatin Kano a kotu
Kungiyar malaman kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, ta baiwa gwamnatin jihar Kano wa’adin mako guda ta daina sayar da filayen makarantar ga jama’a ko kuma ta gurfanar da ita a gaban kotu.
Shugaban kungiyar, Kwamared Ahmad Zubairu Chedi ne ya bayyana haka yau yayin da yake zantawa da manema labarai da ya gudana a kwalejin.
Ahmad Zubairu Chedi ya ce a halin da ake ciki makarantar na fama da karancin gurin da za a fadada gine-gine, don haka ne kungiyar ke kira ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ya ziyarci makarantar don shaida halin da take ciki.
Dakta Chedi ya kuma yi kira ga shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da ya aiwatar da yarjejeniyyar da suka cimma game da walwalar ma’aikata a makarantar ko kuma su tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani nan da mako guda.
Kwalejin Kimiyya dake Dawakin Kudu ta samar da sabon dakin kwanan dalibai
Kwalejin Wasanni ta Jihar Kano Zata Dawo Aiki
kwalejin fasaha ta kano: za mu kara kaimi wajen bunkasa harkokin ilimi
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya rawaito cewa shugaban kungiyar Malaman na Poly Kwamared Ahmad Zubairu Chedi ya kara da cewa tun a watan bakwai na wannan shekarar hukumar kula da ilimin kimiyya da fasaha ta kasa ta amince da a yi musu karin girma duk bayan shekaru uku kamar yadda doka ta tsayar.
Ya kuma ce sabo da haka ne kungiyar ta zauna dan cimma yarjejeniyya game da daukan matakin gaba wanda hakan ne yasa suka yanke hukuncin daukan matakin tsindima yajin aikin nan da kwanaki bakwai in har gwamnati bata biya musu bukatar su.
Ya kuma ce su bawai suna fada da gwamnati bane, a cewar sa kowacce gwamnati tazo za suyi aiki kafada da kafada da ita wajen ciyar da ilimi gaba a jihar Kano.