Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kwallo Kwando: Atlanta Hawks ta sallami mai horar da kungiyar Llyod Pierce

Published

on

Kungiyar kwallon Kwando ta Atlanta Hawks ta raba gari da mai horar da ‘yan wasanta Llyod Pierce, sakamakon rashin tabuka abin a zo a gani da tawagar ke yi.

Gabanin fara gasar kakar wasannin bana ta NBA, tawagar ta Hawks ta dauki dan wasa Bogdan Bogdanovic da Danilo Gallinari, sai Radon Ranjo da Kris Dunn, a kokarin da tawagar take don samun tagomashi a bana.

Sai dai kungiyar ta samu koma-baya sakamakon jinyar rauni da ‘yan wasan tawagar suka yi da ta sa yanzu haka kungiyar ke mataki na 11, a gasar Eastern Conference.

“Mun godewa Pierce da aikin da ya gudanar a tawagar mu da kuma birnin Atlanta”.

“Da shi da matar sa Melissa mutane ne masu matukar muhimmanci a birnin” in ji shugaban gudanar da tawagar ta Atlanta Hawks, Travis Schlenk.

Ya zuwa yanzu tawagar ta Hawks ba ta bayyana sunan wanda zai maye gurbin mai horarwar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!