Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

AFCON: Babu wani kalubale dan Super Eagles ta bi ta ruwa zuwa jamhoriyar Benin – Pinnick

Published

on

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF Amaju Pinnick, ya ce, shi bai ga wani kalubale ba dan tawagar Super Eagles ta bi jirgin ruwa zuwa jamhoriyar Benin a wasan share fagen gasar cin kofin Afirka da za su hadu.

Mai horas da kungiyar ta Super Eagles, Gernot Rohr ne ya sanar cewa akwai yiwuwar tawagar ‘yan wasan su tafi ta ruwa saboda lalacewar hanyar da ta hada Najeriya da Jamhoriyar ta Benin.

Haka zalika, hukumar ta NFF ta tabbatar da cewa za a buga wasan da Najeriya za ta fafata da Lesotho, a filin wasa na Teslim Balogun dake jihar Lagos.

Super Eagles dai za ta barje gumi da Crocodiles a rukunin L a wasannin na share fagen gasar cin kofin na Afirka, a ranar 30 ga watan Maris din shekarar 2021.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!