Labarai
Kwamatin amintattu na jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ya yi watsi da rahoton kwamatin sasantawa

Kwamatin Amintattu na jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya yi watsi da rahoton kwamatin sasantawa da aka kafa domin haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar a ƙasa baki ɗaya.
A cewar rahotonni, kwamatin ya bayar da shawara a ranar Alhamis cewa a dakatar da babban taro na Ibadan har sai an samu cikakken umarnin kotu da ya ce a yi hakan da kuma goyon hukumar zaɓe ta Inec.
Sannan kwamatin, ƙarƙashin jagorancin Hassan Adamu, ya bayar da shawarar kafa kwamatin riƙon ƙwarya na shugabanci saboda yawan umarnin kotuna masu karo da juna kan babban taron.
Sai dai wata sanarwa da shugaban kwamatin amintattun, Sanata Adolphus Wabara, ranar Juma’a ya ce shawarwarin da kwamatin sasantawar ya bayar ba su dace da matsayar shugabancin jam’iyyar ba.
You must be logged in to post a comment Login