Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

PDP ta caccaki ‘yan majalisu kan ciyo bashi

Published

on

Jam’iyyar PDP ta yi Allah wadai da yadda ‘yan Majalisar dokokin kasar nan suka amincewa gwamnatin tarayya ta ciyo bashin dala biliyan 22 da miliyan 7.

A yayin sahalewa karbo bashin, yan Majalisar sun ce sun yi la’akari da rahoton kwamatin Majalisar kan kula da basuka na cikin gida da na kasashen ketare.

Shugaban kwamitin Clifford Ordia ne ya karanto rahoton kwamitin, wanda la’akari da shine kuma Majalisar ta sahalewa Gwamnatin tarayya ta karbo bashin.

Babu banbanci tsakanin jam’iyyun APC da PDP –Bashir Jantile

PDP ta bukaci a sauke hafsodhin tsaron Najeriya bisa gazawar su

PDP:Ta kalubalanci hukumar INEC da zargin sanya rashin kammala zabuka a garuruwan da suke da nasara

Sai dai jam’iyyar PDP ta kalubalanci mambobin Majalisar da amincewa da karbo bashin duk kuwa da yadda al’ummar Najeriya suka nuna rashin amaincewar su.

Wannan kuwa na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun jam’iyyar na kasa Kola Ologbodiyan.

Ta ce ‘yan Majalisar dattijai sun yi gaban kansu wajen amicewa da karbo bashin duk kuwa da cewa fadar shugaban kasa ta gaza bayar da cikakkun bayanai kan yadda za’a karbo bashin da kluma hanyoyin biyan sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!