Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro – An kama gawurtaccen mai safarar makamai a Zamfara

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta kama wani mai suna Ibrahim Adamu da take zargi da safarar makamai, inda ta same shi da kudi naira miliyan daya da zai sayi bindiga kirar AK-47.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar mai dauke da sa hannun kwaminishininta Abutu Yaro, ta ce sun kama Ibrahim Adamu da aka fi sani da Gado bayan samun bayanan sirrin cewa shi da wani fitaccen dan bindiga mai suna Tsoho Dandela suna yunkurin sayen bindiga a hannun shahararren dan bindigar nan mai suna Dogo.

Ta cikin sanarwar, kwamishinan ya ce sun yi nisa cikin binciken da suke gudanarwa, domin samun damar kama sauran ‘yan bindigar da suka addabi al’ummar jihar Zamfara da kewaye.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!