Kiwon Lafiya
Kwamitin bincike tare da biyan kudin tsoffin ma’aikatan kamfanin jirgin sama ya dakar da biyan ma’aikatan
Kwamitin da shugaban kasa kan bincike tare da biyan kudin tsoffin ma’aikatan kamfanin Jirgin Sama na kasa Nigeria Airways, ya ce an dakatar da biyan kudin da shugaban kasa ya sahale wato Naira Biliyan 22 da miliyan 6 sakamakon matsalar da aka fuskanta ta tantance ma’aikatan.
Mataimakin daraktan Kwamitin Mista John Waitono ne ya bayyana hakan yau a Lagos, yayin antawa da manema labarai.
Tun a ranar 15 ga watan Oktoban da muke ciki ne aka fara tantancewar har zuwa jiya 28 ga watan na Oktoba, a cibiyoyi uku na kasar nan da suka hadar da Lagos da Enugu, da kuma nan Kano.
Ya kara da cewa sun shirya fara biyan wadanda aka kammala tantancewa kudadensu bayan ware mutane dubu dai-dai, a wurare daban-daban, sai dai sun dakatar da hakan bayan gano cewa da dama daga cikin ma’aikatan sun halarci wuraren tantancewa fiye da wuri guda.