Labarai
Kwamitin binciken badakala a EFCC ya sami karin hurumi
Kwamitin fadar shugaban kasa dake binciken ayyukan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya samu karin hurumin yin shari’a a wani bangare na fadada ayyukansa.
Shugaban kwamitin mai shari’a Ayo Salami wanda kuma shi ne tsohon shugaban kotun daukaka kara, ya ce mambobinsa za su gudanar da aikin su karkashin sashe na 1 bisa dokar da ta kafa irin wadannan hukumomi ta shekarar 2004.
An umarci kwamitin da ya gabatar da zaman tattaunawa a bainar jama’a, wanda tuni aka fara irin wannan ta na’urar Camera a fadar shugaban kasa.
Ana sa ran kwamitin zai mika da rahoton bayanan da ya tattara bayan kwanaki 45 da gudanar da taron da zai yi a bainar jama’a.
Idan ba a manta ba dai, kwamitin na duba ayyukan mai rikon mukamin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu daga shekarar 2015 zuwa 2020 bayan dakatar da shi.
You must be logged in to post a comment Login