Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

NCDC : Sabbin masu dauke da cutar Korona sun kai 437

Published

on

Cibiyar dakile yaduwar cututka ta kasa NCDC ta sanar da karin sabbin mutane 437 da suka kamu da Annobar cutar COVID-19 a jiya Lahadi.

A sanarwar da cibiyar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce yanzu haka adadin mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya ya kai 46, 577, inda aka sallami 33, 186 daga cikin su bayan tabbatar da sakamakon gwajin da aka yi musu cewar sun warke.

Ya zuwa yanzu dai cibiyar ta NCDC ta ce mutane 945 ne suka mutu a sanadiyyar cutar ta COVID-19.

Cibiyar ta bayyana cewa jihohi 17 ne cikin tarayyar kasar nan aka samu karin masu dauke da cutar.

Anan jihar Kano kididdigar gwajin cutar a jiya Lahadi na nuni da cewa, an samu karin mutane 4 da suka kamu da cutar, wanda ya zamana adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 1, 626.

Rahotanni na nuni da cewa, mutane 1, 308 ne aka sallama bayan gwajin da aka yi musu ya tabbatar da basa dauke da cutar, inda kuma mutane 54 suka mutu a sakamakon cutar ta COVID-19 a fadin jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!