Connect with us

Labarai

Kwamitin CPAC ya bukaci a gurfanar da El-Rufai a kotu ko kuma a sake shi

Published

on

Kwamitin hadakar kungiyar samar da cigaban siyasa ta kasa CPAC ta bukaci gwamnatin tarayyar da ta gaggauta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a kotu ko kuma ta sake shi nan take, tana mai gargadin cewa tsare shi fiye da wa’adin da doka ta amince zai saba wa kundin tsarin mulkin kasa.

 

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin shugabanta ta Aminu Datti-Ahmed, inda ta ce El-Rufai ya amsa gayyatar  Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC tun a ranar 16 ga watan Fabrairu. 

 

Daga baya kuma aka mika shi ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC domin ci gaba da bincike kan zargin badakalar kudi.

 

Kungiyar ta ce umarnin tsare shi na kwanaki 14 ya riga ya kare, don haka dole ne gwamnati ta gurfanar da shi a kotu idan akwai hujja ko kuma ta sake shi, tana mai jaddada cewa Najeriya kasa ce mai bin doka kuma ba za a yi amfani da tsare mutane domin siyasa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!