Labarai
Kwamitin Majalisar Dattawa ya yi barazanar kama tsoffin manyan jami’an NNPCL

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da asusun gwamnati ya yi barazanar kama wasu tsoffin manyan jami’an kamfanim mai na NNPCL bisa zargin rashin bayyana yadda aka kashe kimanin Naira tiriliyan 210 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023.
Kwamitin ya gayyaci tsohon babban Daraktan kamfanin, Mele Kyari, tare da tsohon babban jami’in kudi, Umar Ajia Isa, da kuma tsohon babban manajan zuba jari, Bala Wunti.
Shugaban kwamitin, Aliyu Wadada ne ya bayar da wannan gayyata a ranar Alhamis bayan kwamitin ya duba rahotannin binciken kudi da suka shafi kamfanin mai na kasa.
Aliyu Wadada yayi gargadin cewa kwamitin na da ikon amfani da karfinsa na doka domin tilasta wa tsoffin jami’an su halarci zaman idan har suka ki amsa gayyatar.
Kwamitin ya kuma bayyana cewa zai iya fitar da sammacin kama su idan suka gaza bayyana a ranar da za a sanar nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login