Connect with us

Kiwon Lafiya

Kwamitin shugaban kasa da ke sanya ido don Kawo gyara zai gayyaci gwamnan jihar Gombe

Published

on

Kwamitin shugaban kasa da ke sanya ido don kawo gyara kan ayyukan ‘yan sandan sashen yaki da ‘yan fashi da makami wato Presidential Investigation Panel on the Special Anti-Robbery Squad, ya ce zai gayyaci Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo don yi masa karin haske game da mutuwar wani mai dafa masa abinci.  

Shugaban kwamitin Tony Ojukwu ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja

A cewar sa daukar matakin ya biyo bayan wasikar da wata mata mai suna Mrs Okon ta rubutawa kwamitin ta hannun wani ofishin lauya mai suna Sunny Olorunmola game da mutuwar mai gidan ta mai suna John Okon wanda kuma mai dafa abinci ne na musamman ga Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo.

Tun da farko dai matar ta yi korafin cewa mai gidan na ta ya mutu ne sakamakon dan karen duka da ya sha da kuma azabtar da shi da jami’an ‘yan sandan sashen yaki da fashi da makami wato SARS su ka yi.

Takardar korafin ya kuma ce lamarin ya samo asali ne sanadiyar barayi da su ka shigo gidan Dankwambo da ke Kaduna su ka yi sata, shi kuma John Okon da iyalansa suna rayuwa ne a wani bangare na gidan, wanda a dalilin haka ne aka zarge su da hannu cikin lamarin duk da cewa tun da fari su suka kai lamari gaban ‘yan sanda.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,434 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!