Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Jami’ar Jigawa ta Sule Lamido ta lashe gasar mahawara jam’io’in Afrika ta Kudu

Published

on

Jami’ar jihar jigawa ta Sule Lamido ta sami nasarar lashe gasar mahawara ta Jami’o’in kasashen Afrika ta Yamma  karo na 2 ta bana.

Jami’ar ta Sule Lamido dake Kafin Hausa ta sami nasarar ne a yayin gasar da aka yi a kasar Ghana da aka yi a tsakanin ranar 7 zuwa 11 ga wnnan watan da ya hada da kasashen Ghana da jamahuriyyar Benin da kuma nan Najeriya.

Ana dai gabatar da gasar kamar yadda ake yi  majalisar dokokin  Burtaniya, yayin da za’a sanya mutum hudu su zama masu tafiyar da gwamnati yayin da ‘yan adawa kuma za su tafka mahawara kan kudirin da gwamnatin ta gabatar, kafina yankin hukunci dafa karshe bayan kudirin ya tsallake karatu 5 an kuma tafka mahawara.

Jagoran Tawagar daliban jami’ar ta Sule Lamido da suka wakilci Najeriya a yayin gasar sun hada malaman Idris Hamza Yana da kuma daliban sun hada da Aisha Goni da Alhassan Tsalhatu da Haruna Abdurrahaman da Ibrahim Hussaini Yakubu Da yake tarbar daliban bayan sun dawo daga gasar Shugaban jami’ar farfesa Lawan Sani Taura ya taya su murna saboda jajircewar da suka yi, yana mai cewar kasancewar su jakadu na gari hakan zai dauka jami’ar kai wa mataki na gaba

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!