Connect with us

Labarai

Kwamitin yaki da Daba na Kano ya sake cafke mutane 31

Published

on

Kwamitin da Gwamnatin Kano ta kafa na magance ayyukan Daba da shaye-shaye da kuma dawo da zaman lafiya, ya cafke karin wasu mutane 31 da ake zargi da aikata Daba da kuma masu sayar da miyagun ƙwayoyi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke ganawa da manema labarai a ofishin Anti Daba da ke Tal’udu da yammacin jiya Juma’a.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, kwamitin karkashin jagorancin Dakta Yusuf Ibrahim Kofar mata, ya gudanar da Kamen ne a unguwannin Kofar mata da Sharada da Dorayi da Unguwar Daɓai da sauransu, inda aka gurfanar da mutane 25a gaban Kotu yayin da sauran ke hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA domin faɗaɗa bincike.

Haka kuma SP Kiyawa, ya ce, tawagar jami’an da suka gudanar da aikin sun haɗa da Ƴan sanda da na NDLEA da Civil Defence da na hukumar lura da shige da fice da jami’an hukumar kare afkuwar hadurra da sauransu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!