Labarai
Kwana daya da harin Bagwai, ‘Yan bindiga sun kara kai hari a Danbatta
Wasu ‘Yan bindiga sun harbe mutane biyu a garin Sansan da ke yankin karamar hukumar Dambatta a nan jihar Kano.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun afka gidan Alhaji Abdullahi Sansan inda su ka harbe mutane biyu.
Babban ‘Da’ ga Alhaji Abdullahi Sansan, wato Ado Abdullahi Sansan, ya shaidawa Freedom Rediyo cewa, a daren jiya ne ‘yan bindigar wadanda ake zargin ‘yan fashi ne suka afka musu tare da daure mahaifinsu.
Sai dai ya ce babu wanda ya rasa ransa cikin mutane ukun da aka harba.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan kisan mutane uku da wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne su ka yi a kasuwar Bagwai da ke karamar hukumar ta Bagwai tare da jikkata Mutum guda.
Karin labarai:
Yan bindiga sun hallaka mutane a Kano
‘Yan bindiga sun yi awan gaba da wasu tagwaye
Freedom Rediyo ta tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna kiyawa ya kuma ce ya zuwa yanzu suna kan tattara bayanai amma da zaran sun kammala zai sanar da manema labarai
You must be logged in to post a comment Login