Labaran Kano
Yan bindiga sun hallaka mutane a Kano
Rundunar’yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun hari garin Bagwai dake nan Kano.
Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Kano DSP, Abdullahi Haruna Kiyawa , ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce suna cigaba da bincike.
Rahotonni sun ce maharan sun farwa garin da harbe-harben bindiga inda suka hallaka mutane tare da raunata wasu.
‘Yan bindigar sun shiga garin na Bagwai ne cikin mota da misalin karfe 10:30 na daren jiya Litinin.
‘Yan bindigar sun hallaka wata ‘yar gidan da suka kai harin wadda take jigo a jam’iyyar PDP Hajiya Balaraba Sani.
Daga nan ne kuma suka harbe wani mutum mai suna Muhammad Sani.
Karin labarai:
Operation Puff-Adder sun farwa ‘yan bindiga dadin na Ansaru a dajin Koduru a Kaduna
You must be logged in to post a comment Login