Labaran Kano
Kwankwasiyya ta kara daukar nauyin dalibai don yi karatu a kasashen waje
Gidauniyar ilimi na Kwankwasiyya a jihar Kano ya dauki dauyin dalibai tara ‘yan asalin jihar Kano don yin karatu a wasu zababbun jami’o’I dake kasashen Sudan da hadaddiyar Daular Larabawa.
Dayake jawabi ga daliban jagoran darikar Kwankwasiyya tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwasiyya y ace wadanda suka cigajiyar shirin na daga cikin dalibai 370 da gidauniyar ta kwankwasiyya ta dauki nauyi don yin digiri na biyu a wasu zababun jami’o’in a kasar India da sauran kasashen duniya.
A cewar jagoran na Kwankwasiyya wannan rana ce ta tarihi da baza’a taba mancewa da shi ba, kasancewar gidauniyar ta cika alkawarin ta na daukar nauyin daliban don yin karatu a kasashen waje.
Kamfanin dilancin labaru ta kasa ta rawaito cewar, tsohon shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheik Aminu Ibrahim Daurawa ya gargadi dalibai da su guji take dokokin da hukumomin kasashen da suka je don neman ilimi suka shinfida da kuma aikata miyagun dabi’u.