Connect with us

Labaran Kano

Hukumar Hisbah ta Kano ta cimma yarjejeniyar aiki da KAROTA

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano da na KAROTA sun kammala cimma yarjejeniyar hada hannu don tabbatar da cewa masu ababan haw ana bin ka’idojin hanya bda toki a ciki da wajen birnin Kano.

Babban kwamnadan hukumar ta Hisba Sheik Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar aiki ga babban manajan daraktan hukumar ta KAROTA Alhaji Baffa Babba Dan Agundi a offishin sa.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na Hukummar Hisba Lawan Ibrahim Fagge ya fitar cewa, shugaban hukumar ta Hisbah Harun Ibini Sina suna da nasaba ta aiki da na KAROTA Baffa Babba Dan Agundi wajen tabbatar da zaman lafiya da bin ka’idojojin aiki ta hanyar kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Kano baki daya.

Hukumar Hisbah ta gana da saurayin dake shirin auren Ba’amurkiya

Hisbah zata bude sabbin ofisoshi a Kano

Da dumi-dumi: Hisbah ta janye dokar hana cakuda maza da mata

Da yake jawabi shugaban na KAROTA Babba Dan Agundi ya bayyana ziyarar da hukumar ta Hisbah ta kawo masa a matsayin abun a yaba, yana mai cewar, nan bada jimawa ba hadin gwiwar zai fara aiki  don tabbatar da al’ummar jihar Kano na bin ka’idojojin aiki.

Shugaban na KAROTA ya kuma yabawa masu ababan hawa da matoka wajen marawa hukumar ta KAROTA baya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,751 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!