Labarai
Kwankwaso na nan Daram a NNPP- Hashimu Dungurawa

Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen shekarar 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma jam’iyyar African Democratic Congress ADC.
Dungurawa, yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Litinin, ya bayyana cewa Kwankwaso ba ɗaya ba ne daga cikin ’yan siyasar da ke yanke shawara cikin gaggawa ba tare da zurfin tunani da la’akari da sakamakon hakan ba.
A cewarsa, Kwankwaso shi ne jagoran siyasa a arewacin Nijeriya, inda ya kara da cewa “kowanne dan siyasa kokari ya ke Kwankwaso ya shigo jam’iyyar su, to ta yaya za a ce wai zai koma ADC.
You must be logged in to post a comment Login