Connect with us

Coronavirus

Kwankwaso ya bayar da gudummuwar Asibitinsa kan Coronavirus

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankawaso ya bawa kwamatin yaki da cutar Corona na jihar Kano Asibitinsa na Amana a matsayin gurin da za’a rinka killace wadanda suka kamu da cutar Coronavirus.

Mataimaki na musamman ga tsohon gwamnan Rabi’u Kwankwaso kan kafafen sadarwa na zama ne Saifullahi Hassan ne ya bayyana hakan ga Freedom Radiyo ta cikin wani sakon murya daya turo mana.

Inda yace a yau Litinin Rabi’u Kwankwaso ya sanar da mallakawa gwamnatin ta Kano Asibitin nasa na Amana dake Titin Milla a unguwar Nasarawa dake nan Kano, domin yaki da wannan annoba.

Saifullahi Hassan ya kuma ce yanzu haka Asibitin na dauke da gadaje guda sittin da biyar da za’a iya kwantar da marasa lafiya akai.

Ya kuma ce ya bayar da asibitin ne biyo bayan halin da al’ummar jihar Kano suka tsinci kansu game da annobar Corona data bulla a jihar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,465 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!