Connect with us

Coronavirus

Jami’an tsaro su kara kaimi a bakin aikin su -Baffa Babba

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano Karota ta bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi a kan aikin su musamman ma a kan bakin shingayen kan hanya da a ka umarce su.

Shugaban hukumar, Dakta Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan  cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabulisi Abubakar ya sanyawa hannu.

Ya kara da cewar gwamnatin jihar Kano ta dauki matakin ne domin ganin komai na tafiya bisa ka’ida tare da hana zirga-zirga a kan hanya wanda hakan shi ne hanyar magance yaduwar cutar a Kano.

Baffa Dan Agundi ya yi kira ga iyaye dasu kula da ‘ya’yan su saboda wasan kwallon kafa da yaran su ke gudanar da wasan a kan titina maimakon hakan su fadakar da su illar yin hakan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!