Labaran Wasanni
Kyaftin ya samu nasarar daukar Kofi bayan shekaru 15 ba tare da Nasara ba
Kyaftin din kungiyar Kwallon kafa ta Dakata Warriors Kabiru Muhammad, ya samu nasarar lashe kofin hadin kan Dakata wato Dakata Unity Cup, bayan shafe shekaru kusan sha biyar ba tare da daukar wani Kofi ba.
Kyaftin Kabiru, wanda ya jagoranci kungiyar sa ta Dakata Warriors wajen doke takwarar ta, ta Dambo Dawaki, da ci daya da nema, a wasan karshe na gasar ya bayyana jin da din sa, musamman ma ta hanyar hada kan matasa da zumunci da gasar ta hada, da uwa uba kuma shekarun da ya diba ba tare da daukar Kofi ba.
Tun da fari, dan wasan Dakata Warriors Odey Joseph, ne ya zura Kwallo daya tilo a minti na 25, na farkon Rabin lokaci, wanda aka tashi wasan a haka.
A nasa jawabin, wanda ya shirya gasar Coach Mustapha Ajasco, ya ce zai cigaba da hadawa tare da daukar nauyin gasar don hada zumunci tsakanin matasan yankin, da samar musu da abun yi a fadin jiha.
Gasar dai, an karkare ta da raba kyaututtuka, da suka hada da karrama manyan baki, sai wanda ya fi kowa zura Kwallo Naziru Noti, mai Kwallo takwas, dan wasa mafi hazaka a gasar Umar Yahuza daga Koncieslney Fc, mai tsaron raga da ya fi kowa hazaka Khamisu daga Dakata Warriors, sai mai horar wa da aka zaba yafi kowa, Coach Cisse daga kungiyar Sauna Pillars.
An dai karkare gasar, cikin kade-kade da nishadi, wacce ta samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban, da dumbin ‘yan kallo da suka halarci gasar da ta gudana a filin wasa na Kungiyar Kwallon kafa ta Mancity Dakata, dake makarantar Sakandiren Kawaji, a unguwar Dakata.
You must be logged in to post a comment Login