Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Yanzu-yanzu: Dan wasan Nasarawa Utd ya mutu ana tsaka da wasa

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Nasarwa United dake birnin lafiya, ya rasu a filin Kwallo yayin da ake tsaka da wasa, bayan sun yi taho mu gama da dan wasan kungiyar Katsina United a wasan Firimiya ta kasa mako na 23.

Dan wasa Chieme Martins, ya mutu nan take a filin wasa duk da kokarin da akayi na a samu ceto shi daga buguwar da yayi a kansa, amma hakan ya ci tura kafin daga baya, ya rasu.

Wakilin mu Aminu Halilu Tudun wada ya rawaito mana cewa ana kokarin garzaya da shi zuwa Asibiti Jim kadan bayan faduwar sa, amma kasancewar rasuwar tashi ta tsaida yunkurin tafiya can don ceton ran nasa.

Wasan dai Kungiyar Nassarwa United ta samu nasara da ci uku da nema akan Katsina United, inda dan wasa Ohanocham, ya zura kwallaye uku a mintina na 50, 61 da 88.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!