Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kylian Mbappe da Neymar sun taya Bayern Munich murna

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta PSG, Kylian Mbappe da Neymar Junior sun ta ya kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich murnar lashe kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafar Turai wato Champions League.

A daren jiya Lahadi dai kungiyar ta Paris Saint-Germain ta yi rashin nasara a hannun Bayern Munich da ci 1-0, wanda hakan ya baiwa Bayern damar daukan gasar.

A mintina na 59 bayan dawowa daga hutun rabin Lokaci tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafar ta PSG Kingsley Coman da ya sauya sheka zuwa Bayern Munich ya zura kwallo dayan data baiwa kungiyar nasarar lashe kofin.

Nasarar cin kwallon da Kingsley Coman ya yi ya sanya ya zama dan wasan kasar Faransa na biyar da ya ta zuwa kwallon a wasan karshe a gasar cin kofin na zakarun Turai cikin yan wasan kasar da suka halarci wasan karshe a gasar.

Wannan dai shi ne dai karon farko da kungiyar ta PSG tazo wasan karshe a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafar ta Turai.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!