Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Laifin Fyade: An yankewa wani matashi hukunci ɗaurin shekaru 14

Published

on

Babbar kotun Jihar Kano mai zamanta a Miller Road karkashin mai shari’a Sulaiman Baba Na-Malam ta yankewa wani mutum mai suna Yusuf Muhammad hukuncin daurin shekaru 14.

Kotun ta kuma ce zai biya tarar naira dubu dari biyu bayan samunsa da laifin aikata fyade.

Kotun ta ce a ranar 10 ga watan Nuwambar shekarar 2017 ne Yusuf Muhammad da ke zaune a karamar hukumar Gwarzo ya yaudari wata yarinya mai shekaru 8 har yayi mata fyade a wani gidan kallon kwallo.

Yayin zaman Kotun, mai gabatar da kara lauyan gwamnati Barista Ali Yusuf Kabara, ya gabatar wa kotu shaidu bakwai, inda wanda ake tuhuma ya kare kansa da kansa.

Tuni dai mai shari’a Sulaiman Baba Na-Malam ya bayyana cewa aikata fyade a jihar Kano ya saba da dokokin kundin Penal Code.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!