Labarai
Laifin makara: Gwamnatin Gombe ta dakatar da ma’aikata 731
Gwamnatin jihar Gombe ta dakatar da albashin ma’aikatan ta 731 sakamakon makarar su zuwa wajen aiki.
Wadanda aka kora an kama su da laifin makara a watan satumbar da muke ciki.
Kwamishinan kudi da tattalin arziki na jihar, Muhammad Gambo Magaji ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai.
Ya ce, yanzu haka wasu mutane 170 da ake zargi da rashin zuwa aiki ana kan bincikar su.
Muhammadu Gambo Magaji, ya ce gwamnatin jihar ta samu rarar kudi da suka kai kimanin miliyon 57 da dubu dari 6 na ma’aikatan jihar da na kananan hukumomin da aka dakatar da albashin na su.
You must be logged in to post a comment Login