Labarai
Lassa tayi asarar rayuka a jihar Gombe
Gwamnatin jihar Gombe ta tabbatar da rasuwar mutane uku a sanadiyar kamuwa da cutar zazzabin Lassa.
Kwamishinan lafiya na jihar Gombe Dakta Ahmad Muhammad Gana ne ya bayyana hakan a yau Talata ya yin da yake ganawa da manema labarai kan bullar cutar Lassa a jihar.
Dakta Gana ya ce mutane bakwai ne suka kamu da cutar inda uku daga ciki suka rasa rayukansu.
Zazzabin Lassa ya barke a jihar Kaduna
Likitocin AKTH sun rasa rayukan su saboda zargin kamuwa da zazzabin Lassa
Sarkin Kano ya ankarar da jama’a kan cutar Lassa
Kazalika Dakta Gana ya ce tuni gwamnan jihar Gombe ya bada umarnin killace sauran mutane hudu da suke dauke da cutar don cigaba da kula da lafiyarsu.
Wakilin mu Sa’idu Baffa Malala ya rawaito cewar, wadanda suka rasu, mutum guda ya fito ne daga Karamar hukumar Ibbi ta jihar Taraba sai kuma daya daga karamar hukumar Bayo ta jihar Borno sannan mace daya daga Yamaltu Deba a jihar Gombe.