Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano zata  sanya kafar wando daya da wata Baturiya

Published

on

Kwamishiniyar ma’aikatar al’amuran mata da walwalar jama’a Dr. Zahra’u Muhammad Umar ta ce, ma’aikarata za ta sanya kafar wando daya tsala da wata Baturiyar kasar Nethtland mai suna Foyna  wacce ta shafe shekaru 13 a nan Kano.

Baturiyar wacce take bude wani gidan yara mara sa galihu kamar su almajirai dama sauran yaran da yake ya dai daita da ake dibansu daga garuruwan Maiduguri Yobe ana kawowsu na jibgewa

yayin da ta bude wani waje a gidan ta dake Hotoro, kuma ta sanya malamai su na basu karatu sai dai akwai tarin matsaloli da aka gano su na faruwa a gidan ta.

Wani matashi mai bibiyar harkokin yau da kullum  da ya yi bincike mai tsaye kan wannan gida, daya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewar, har yanzu akwai yara a gidan Feyona, duk da umarnin da ma’aikatar mata da jin dadin walwalar jama’a  ta Kano ta  bayanna rufe wannan gida amma ita Fyona ta yi kunna uwar shegu da wannan gargadi.

Dr. Zahra’u Muhammad Umar ita ce kwamishinan yara harkokin mata da walwala ta jihar Kano ta ce, dama su na sane da wannan mata Feyona kuma suna bincike a kanta kuma da zarar bincikenta ya nuna a kanta za su dauki matakin da ya dace akan wannan mata Foyena.

Dole ne na maida da na makarantar ‘Yan Mari-Mahaifi

Hukumar Hisbah ta ziyarci makarantar ‘yan mari ta zamani

Wasu ‘yan Mari sun farwa malaman su

Filin Inda ranka ya yi kokarin jin ta bakin wannan mata Foyana tunda ya ke akwai hakkin fadin albarkacin baki amma ba mu samu damar jin ta bakin ta, kuma filin Inda Ranka ya yi kokarin jin ta bakin hukumar kula da shige da fice ta kasa reshan Kano, wato Immgration dan jin shin wannan mata tana da cikakkun shedun zaman kasar nan .

Amma basu bamu ba, kuma izuwa yanzu akwai wata Magana akan gidan Foyana a gaban hukumar Naptip, wanda shima duk zamu bibiya zuwa gobe itama idan na sameta a goben zamu ji ta bakin ta .

Har lla yau kwamishiniyar harkokin mata ta jihar kano Dr. Zaharu Umar ta ce, nan gaba kadan za su jere yaran da su ka gano a wani gida a sabon gari da ake zargin wani Profeson gobe ya boye yana koya musu saka da mugun zare domin al’umma su gansu ko Allah ya sa a gano iyayensu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!