Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Lassa tayi asarar rayuka a jihar Gombe

Published

on

Gwamnatin jihar Gombe ta tabbatar da rasuwar mutane uku a sanadiyar kamuwa da cutar zazzabin Lassa.

Kwamishinan lafiya na jihar Gombe Dakta Ahmad Muhammad Gana ne ya bayyana hakan a yau Talata ya yin da yake ganawa da manema labarai kan bullar cutar Lassa a jihar.

Dakta Gana ya ce mutane bakwai ne suka kamu da cutar inda uku daga ciki suka rasa rayukansu.

Zazzabin Lassa ya barke a jihar Kaduna

Likitocin AKTH sun rasa rayukan su saboda zargin kamuwa da zazzabin Lassa

Sarkin Kano ya ankarar da jama’a kan cutar Lassa

Kazalika Dakta Gana ya ce tuni gwamnan jihar Gombe ya bada umarnin killace sauran mutane hudu da suke dauke da cutar don cigaba da kula da lafiyarsu.

Wakilin mu Sa’idu Baffa Malala ya rawaito cewar, wadanda suka rasu, mutum guda ya  fito ne  daga  Karamar hukumar Ibbi ta jihar Taraba sai  kuma daya daga karamar hukumar Bayo ta jihar  Borno  sannan mace daya daga Yamaltu Deba a jihar Gombe.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!