Kiwon Lafiya
Likitoci sun janye yajin aiki
Gamayyar Kungiyar likitoci ta kasa ta ce ta dakatar da yajin aikin da ta tsunduma a makon da ya gabata, bayan da shugaban majalisar dattijai ya shiga tsakani.
Sai dai ta ce matukar gwamnatin tarayya bata biya mata bukatun ta ba nan da makonni 4 masu zuwa to kuwa tabbas zata sake tsunduma yajin aiki.
Shugaban kungiyar na Asibitin Aminu Kano Dakta Abubakar Nagoma Usman ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da Hantsi na nan tashar Freedom Radiyo da ya mayar da hankali kan yajin aikin da likitoci masu neman kwarewar suka tsunduma.
Rahoto: Likitoci a Kano sun tsindima yajin aiki
Dalilin da ya sanya jami’an KAROTA basu fito aiki ba – Baffa
Ya ce, tun a baya akwai al’kawuran da gwamnati ta daukarwa lilkitocina na biya musu kudaden karo karatu, da biyan su alawus-alawus din su, da kuma dawo da ma’aikatan asibitin koyarwa na jami’ar jos da aka kora daga bakin aikin su da sauran bukatu.
Dakta Abubakar ya ce har yanzu da gwamnati ke ikirarin ta samarwa da likitoci kayan kariya daga cutar Corona kungiyar su bata samu Kayayyaki ba, kuma babu wani tallafi, sai dai zasu ci gaba da bibiya don ganin kayan sun zo gare su.
Dakta Abubakar ya ce har yanzu da gwamnati ke ikirarin ta samarwa da likitoci kayan kariya daga cutar corona kungiyar su bata samu wannan tallafi na azo a gani ba, a don haka kungiyar zata ci gaba da bibiya don ganin an cika musu alkawuran su.
You must be logged in to post a comment Login