Connect with us

Labaran Wasanni

Dalilan da suka sanya Real-Madrid ta zama ta daya a gasar Laligar kasar Spaniya

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Real-Madrid ta zama ta daya a gasar Laligar kasar Spaniya, bayan ta samu nasara kan kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad  da ci biyu da daya a daran jiya.

Yanzu dai Madrid ta yi kankankan da Barcelona wajen maki a gasar ta Laliga, inda ko wacce kungiya ke da maki 65.

A ranar juma’ar data gabata ne dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tai canjaras da Sevilla ko wacce na nema 0-0, wanda hakan ne ya baiwa Madrid damar zama ta daya a gasar, bayan nasarar data samu a jiya Lahadi kan Real Sociedad.

Dalilan da suka sanya Real-Madrid ta zama ta daya a gasar ta Laliga duk da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fita yawan zura kwallaye a raga.

Yanzu dai Barcelona nada kwallaye 38, inda Real Madrid ke da kwallaye 36.

Kamar yadda yake a tsarin gasar ta Laliga idan kungiyoyi suka yi canjaras ana fara duba kungiyar dataci wata a gasar sai ta zama ta daya.

A bana wasan farko tsakanin Real-Madrid da Barcelona daya gudana a ranar Lahadi 27 ga watan Octoban wasan daya gudana a filin wasa na Santiago Bernebau   inda aka tashi kowacce kungiya na nema.

Sai kuma wasa na biyu daya gudana a ranar 1 ga watan Maris din daya gabata a filin wasa na Comp Nou, wanda Real Madrid ta samu nasara kan Bacerlona da ci 2-0

Nasarar da Madrid ta samu kan Barcelonan a ranar ta 1 ga watan na Maris shine ya bata damar zama ta daya a gasar ta Laliga.

Zuwa yanzu dai an buga wasanni 30 a gasar ta Laliga, inda ya rage wasanni 8 a karkare gasar ta bana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 328,732 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!